Hot Posts

6/recent/ticker-posts

ABIN AL-AJABI

WANNAN LABARIN Abin al'ajabi MAI TSAN TSAN RIKITARWA??? Labarine mai cike da Al'ajabi kuma lallae wannan abu ya faru Zahiri a wani gari kusa da babban birnin tarayya, Abuja sai dai Labarin yana dan tsawo kadan.. Wata rana, wani mutum matafiyi ya yada zango a wani Masallaci aka gabatar da Sallar Magriba tare da Shi. Da aka idar da sallar, sai ya tashi ya bayyana wa jama'a cewa shi matafiyine, kuma yana cikin halin neman taimako saboda guzurinsa ya kare baki daya, ga shi tafiyarsa mai nisa ce, daga wannan garin mai makwabtaka da Abuja Sakkwato yanufa, a cewarsa. Bayan ya kammala gabatar da kokensa, nan take aka tara masa kudi daidai gwargwadon hali. Bayan an tattara an mika masa wannan kudin, sai kuma ya nemi alfarmar cewa a barshi ya kwana a cikin masallacin, domin gobe da safe ya yi sammako ya damki hanya tunda dare ya sawo kai a wannan Lokacin. Bayan ya nemi wannan alfarmar, kwamitin Masallaci ya duba bukatarsa sai aka amince masa ya kwana tare da hannanta masa mukullen masallacin. Da asubahi Ladanin Masallacin yaje domin ya kira salla ai sai labari ya sauya, domin koda ya bude sai yaga wannan bawan Allah a mace. "ai ba anan gizo ke sakar ba, wato wani abin al'ajabi shine Gawar mutum an riga da anyi masa sutura sai dai an bar fuskarsa a bude. An yi masa wanka an saka shi a Likafani kuma an sanyashi a Makara sannan kuma aka ajiyeshi a tsakiyar Masallaci. Ladani bai kawo komi a ranshi ba, ya wuce kai tsaye ya kira Sallah sannan ya cigaba da Nafilfilin sa. Haka dai jama'a suka yita taruwa a masallaci. Can da Liman ya iso sai aka shaida masa abinda ya faru kuma babu wanda yasan sanadin mutuwarsa ballantana batun yi masa sutura. Liman yace to a fitar da gawar idan yaso bayan an idar da sallah, sai a sallaceta a kaita. Bayan an idar da sallah ne sai akayita ce-ce ku ce akan wasu na cewa lallae a fara sanar da hukuma tukunna domin aji daidaitar abubuwa. Bayan an sanar da Jami'an Yan sanda, sai DPO ya garzayo domin ya ganema idanunsa wannan alamari. Da DPO ya zama ganau sai yace Lallai wannan gawa sai dai akaita Babban Asibitin kusa dasu domin a adana gawar a Dakin adana gawawwaki domin yin bincike. Ya bada motar yan sanda aka sanya gawar domin tafiya Asibiti. Yan sanda biyu da direba, sai DPO ya bukaci masallaci su bayar da mutane biyu da zasu hadu da yansandan su kai gawar Asibitin. Tun da suka dunguma zuwa asibitin, babban abin tashin hankali da kuma al-ajabin da ya faru shi ne, daga Motar yan sandan, da Yansandan su uku da Wakilan masallacin su biyu har ita kanta gawar har zuwa yau da nake baku labarin ba a sake jin duriyarsu ba, ko sama ko kasa Allahu A-alamun! "Inna lillahi wa'inna ilaihi rajiun" wannan Labari na samo shine a Cikin Jaridar Leadership Hausa. domin samun labaran abubuwan al-ajabi harda ma na abubuwan ku biyomu a wannan shafin

Post a Comment

0 Comments