Hot Posts

6/recent/ticker-posts

Illar gurbatacciyar iska ya wuce yanda muke tinani — Hukumar lafiya ta duniya

Illar gurbatacciyar iska ya wuce yanda muke tinani — Hukumar lafiya ta duniya
Gurbatacciyar iska na janyo dumamar yanayi Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta yi gargadi kan illar da gurbatacciyar iska ke haddasawa, fiye da binciken da akayi a baya, inda ta ce matsalar a halin yanzu ta zarta duk yadda ake hasashe. WHO, ta ce wani kiyasi ya nuna kusan mutum miliyan bakwai ke mutuwa katsahan a duk shekara, sakamakon cututtuka masu nasaba da shakar gurbatacciyar iska. Bincike ya nuna kasashe masu tasowa da matalauta su ne suka fi shan wuyar, saboda dogaron da suka yi da man fetur dan bunkasa tattalin arziki da kudaden shiga. WHO ta kara da cewa gurbatacciyar iska ta fi taba sigari ko rashin abinci mai gina jiki saurin yi wa dan adam illa. WHO, tayi kira ga kasashe 194 da su yi kokarin rage gurbataccen hayakin da suke fitarwa, wanda ke tasiri ga sauyin yanayi gabannin babban taron koli da za a tattauna kan batun a watan Nuwamba mai zuwa. Cikin cututtukan da gurbatacciyar iska ke haddasa wa dan adam akwai ciwon zuciya, da shanyewar barin jiki, da cutar Asma da sauransu. Haka kuma ta na janyowa yara tawaya wajen rage bunkasar huhunsu da matsananciyar cutar Asma. "Ku inganta iskar da ku ke shaka, ku magance sauyin yanayi, ku kokarta rage fitar da gurbataccen hayaki, ita ce sassaukar hanyar magance matsalolin da ka iya zama illa ga rayuwar mutane ," inji WHO.

Post a Comment

0 Comments