Yana Bani Labarin Yana Kuka Nima Ina KukaðŸ˜ðŸ˜
Tunda nayi Aure wallahi matata ce take mini wankin kayana tsahon shekaru 10 kenan.
A duk tsahon lokutannan ban taɓa gode mata ba Idan tayi mini ƙorafi akan hakan sai nace mata ai ibada kike yi ba sai nagode miki ba
Haka take haƙuri ta rabu dani kuma bata daina abinda takeyi ba a wasu lokutan takan nuna mini cewa aƙallah idan nagode mata zataji daɗi. Amma wallahi bana kulata hasalima faɗa nake yi mata.
Sai nace mata zan ƙaro aure tunda ita godiya take buƙata sai tayi dariya tace mini ka ƙaro mana ai ko wacce mace da halinta zata zauna.
Idan ta faɗa mini haka sai na gwaleta nace kishi ne da baƙin ciki yake damunta
Takan yawan faɗa mini cewa Abban (Aisha) ina sonka, Amma banajin daɗin yadda kake mini dan Allah idan nayi maka laifi ne kake mini haka kayi haƙuri
Amma wallahi ko a jiki na.
Wani lokacin takaici yakan sakata tace mini Allah yasa na rigaka mutuwa a lokacin zaka gane irin son da nake yi maka a rayuwa da kuma haƙurin dana keyi da kai, ina mai tabbatar maka ba kowacce mace ce zata iya haƙuri dakai ba.
Ina son na rigaka mutuwa domin bana buƙatar wani namiji ya taɓa jikina ballantana ya Mallake ni a matsayin mata, kai kaɗai nake burin zama dashi a rayuwata.
Yanzu maganar da nake yi maka Allah ya É—auki kayarsa ðŸ˜ðŸ˜ Matata Fatima
Yanzu Nnayi Aure kuma Allah ya buÉ—a mini. Kuma na samu dukiya mai yawa. Matar dana aura kafin a É—aura mana auren sai da na kaita aikin hajji sannan na siya mata motar miliyan biyu nayi mata lefe na gani na faÉ—a.
Abinda yanzu yake damuna a rayuwata shine duk abinda nayi mata bata gode mini. Abinda take nuna mini kullum shine haƙƙin tane. Kuma a gidansu tana samun sama da abinda nakeyi mata, dan haka ba wata bajinta nake yi ba da zata rinÆ™a gode miniðŸ˜ðŸ˜.
Wallahi abin yana damuna ita ko kayan ta bata iya wankewa ballantana nawa.
Duk lokacin dana yi mata abu bata gode mini sa sai na tuna da matata Fatima nace to daman haka take jin zafi a cikin zuciyarta Lallai Fatima jaruma ceðŸ˜ðŸ˜.
0 Comments